Home | About Us | Contact Us | Follow Us On Facebook


Adjectives yana nufin 'siffa' ko kuma 'siffatau' wato kalmomi irinsu 'ugly' (muni) 'beautiful' (kyawu), 'strong' (karfaffa) da dai sauransu

Za'a iya anfani da 'adjective' wajen yin 'comparative' (wato domin nuna yanda abu yafi kau ko yafi muni. Misali 'strong' yana nufin 'mai karfi', sannan kuma 'stronger' yana nufin 'karfaffa'.

Galibi idan 'adjectives' yana da 'syllable' (gabobi) guda daya zuwa biyu ne kawai, ana yin 'comparative' nashi ta hanyar sanya 'er' a karshe, misali

AdjectivesComparative
greatgreater
fastfaster
strongstronger

Amma idan 'adjective' yana da gabobi fiye da biyu, akan yi anfani da kalmar 'more' ne domin yin 'comparative' misali:

AdjectivesComparative
intelligentmore intelligent
Za kuma a iya yin anfani da 'adjectives' domin yin 'superlatives' (wato mataki na uku da yake nuna mafi inganci ko mafi muni (misali 'strong' (karfi), 'stronger' (Karfaffa) da kuma 'strongest' 'mafi karfi'

Galibi idan kalma tanada 'syllable' guda daya zuwa biyu kawai, ana yin 'superlative' nashi ta hanyar sanya 'est' a karshenta. Misali:

AdjectivesComparativeSuperlative
loudlouderloudest
coolcoolercoolest
smartsmartersmartest

Amma idan kalmar 'Adjective' tana da gabobi fiye da biyu, akan mayar da ita zuwa 'superlative' ne ta hanyar yin anfani da kalmar 'most' misali:

AdjectivesComparativeSuperlative
Intelligentmore intelligentmost intelligent

To amma wadansu 'Adjective' din yanayin yanda ake 'comparative' nasu da kuma 'superlative' nasu ya banbanta. Misali:

AdjectivesComparativeSuperlative
goodbetterbest
badworseworst
littlelessleast
muchmoremost
farfurtherfurthest

Aika Zuwa

Facebook Twitter Whatsapp

Home

© Copyright 2014 shamsuddeen inc. All right reserved.